Majalisar Wakilai ta ƙasa ta yanke shawarar fara bincikar yadda aka yi amfani da dala biliyan 1.8 da Dala biliyan 2.8 da Najeriya ta samu daga asusun bada tallafi na da kuma Hukumar USAID suka bayar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
An bayar da wadannan kudade ne domin tallafawa yaki da cututtuka kamar HIV, tarin fuka (TB), da zazzabin cizon sauro (malaria), tare da nufin karfafa tsarin kiwon lafiya a Najeriya.
Sanarwar da mataimakin mai magana da yawun majalisa, Philip Agbese, ya gabatar a zaman majalisa ranar Talata ta bayyana cewa asusun an kafa shi ne a 2002 domin tattara kudade da hanzarta yaki da cututtuka, musamman a yankin Afirka ta Yamma.
Agbese ya ce Najeriya ta samu kusan dala biliyan 1.8 daga asusun, yayin da sama da dala miliyan 2.8 suka iso daga USAID tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024 domin magance cututtuka kamar HIV, malaria, polio, da TB.
Ya kara da cewa shirin gaggawa na Shugaban Amurka na tallafawa yaki da cututtuka (PEPFAR) ya bada sama da dala biliyan 6 ga Najeriya daga 2021 zuwa 2025 domin yaki da cutar HIV/AIDS da karfafa tsarin kiwon lafiya da al’umma.
Duk da manyan jarin da aka yi, Najeriya na fuskantar babban kalubale na lafiyar jama’a, ciki har da mutuwar yara sama da 15,000 saboda cututtuka a shekarar 2023, da mutuwar mutane 51,000 gaba daya, inda kasar ke matsayi na uku a duniya wajen mutuwar masu cutar HIV.
Sakamakon haka, majalisar ta nada kwamitin kula da HIV/AIDS, TB, da malaria domin bincikar yadda aka yi amfani da tallafin daga 2021 zuwa 2025, tare da bayar da rahoto cikin makonni hudu don daukar matakin doka na gaba.













































