Fitaccen malamin addinin musuluncin man Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu

Dahiru Bauchi 750x430

Fitaccen malamin addinin musulunci kuma jagora a ƙasar nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu bayan doguwar jinya.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu da safiyar ranar Alhamis a Cibiyar Koyarwa ta Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Wani ɗan uwan marigayin mai suna Malam Ahmed Mohammed ya tabbatar da rasuwar a Bauchi, inda ya bayyana cewa malam ya karɓi baƙi har daren Laraba kafin daga bisani a kaishe shi asibiti inda ya rasu.

A cewar iyalan, za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a ranar Juma’a, 28 ga Nuwamba, a Bauchi bisa tsarin shari’ar musulunci.

Sheikh Usman-Bauchi, wanda mai rikon lambar girmamawa ta (OFR) ne, ya shahara a Najeriya saboda zurfin iliminsa, jagorancinsa da jajircewarsa wajen yaɗa addinin musulunci cikin lumana da fahimtar juna.

An haife shi a shekarar 1927 a Gombe, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta ilimin musulunci, ƙarfafa zaman lafiya da haɓaka haɗin kai a ƙasar nan, tare da jagorantar ƙungiyar Tijjaniyya a Najeriya.

Marigayin ya taka muhimmiyar rawa a ci gaban al’umma, tarbiyyar matasan malamai da kuma bunƙasa fahimtar addini, sannan ya bar ’ya’ya 61 da kuma jikoki da ƴaƴan jikoki da dama.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here