Jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara ta sanar da cewa za ta karrama Alhaji Usman Yahaya Kansila, shugaban kamfanin UYK Consortium, da digiri na girmamawa a bikin yaye ɗaliban ta na farko.
Sanarwar ta fito ne a cikin wata wasiƙa da aka rubuta mai kwanan watan 5 ga watan Nuwamba, 2025, ɗauke da sa hannun rajistarar jami’ar, Ms Olufunke E. Hudson.
Wasiƙar ta bayyana cewa Majalisar Jami’ar da Kwamitin Gudanarwa sun amince da wannan karramawa saboda muhimmiyar gudunmawar da Kansila ya bayar ga ci gaban ilimi a jihar Kogi da kuma fadin Najeriya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa bikin yaye ɗaliban zai gudana ranar Asabar 29 ga watan Nuwamba a harabar jami’ar.
Ms Hudson ta yi bayanin cewa wannan karramawa na nuna godiyar jami’ar ga mutanen da suka jajirce wajen tallafa wa ci gaban ilimi.
Ta kara da cewa wannan girmamawa babbar yabo ce, tare da taya Kansila murna a madadin shugabanci, ma’aikata da ɗaliban jami’ar CUSTECH.
Jami’ar ta tabbatar da girmamawarta ga shugaban kamfanin UYK Consortium sannan ta yi fatan wannan yabo zai ƙara inganta hadin kai domin kara haɓaka ci gaban ilimi a jihar.













































