Cibiyar Kare Hakkokin Dan Adam da Cigaban Jama’a ta yi Allah-wadai da sace ’yan mata 25 daga makarantar sakandaren yan Mata ta Maga a Jihar Kebbi, tare da jaddada cewa bai kamata yara su ci gaba da karatu cikin tsoro ba.
Cibiyar ta bayyana haka ta bakin Daraktan Gudanarwa, Yusha’u Sani Yankuzo, a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a ranar Juma’a.
Yankuzo ya bayyana cewa harin da ya faru da misalin ƙarfe 4 na asuba a ranar 17 ga Nuwamba, 2025, ya sake tunatar da yanayin tabarbarewar tsaro a ƙasar nan.
Ya nuna cewa lamarin maharan da suka kashe Mataimakin Shugaban Makarantar tare da jikkata jami’in tsaro, ya sake tada bakin cikin al’ummar ƙasa, yana tunzura tunanin sace ’yan matan Chibok na 2014.
Ya jaddada cewa abin bai dace ba cewa ’yan mata masu neman ilimi su ci gaba da fadawa hannun miyagun da ke aikata ta’addanci.
Ya gargadi cewa irin wadannan hare-hare suna kara rage amincewar jama’a ga tsaron kasa tare da barazana ga makomar yaran Najeriya.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali daga siyasa zuwa kan matsanancin yanayin rashin tsaro, dominkariya ga ’yan kasa nauyi ne da kundin tsarin mulki ya tanada a sashe na 14(2)(b) na kundin tsarin mulki na 1999.
Ya kara da cewa yawaitar sace mutane, ta’addanci, da hare-hare na nuna cewa akwai bukatar tsari mai karfi da ya hada kai wajen inganta tsaron kasa.
Sanarwar ta bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi, su karfafa tattara bayanan sirri, tare da tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata wannan ta’asa ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce al’ummomi da sarakunan gargajiya su sami cikakken tallafi domin inganta hanyoyin gargadi da tsaron yankuna.
Cibiyar ta mika ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da al’ummar Jihar Kebbi baki daya, tare da jaddada cewa ba ɗaiyar yaro ya kamata ya yi karatu cikin tsoro ba.













































