Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin zamanantar da Green Park

FB IMG 1782559815458 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa aikin sake gyara Green Park da ke kan Titin Audu Bako ya kusa kammala, wanda hakan ya nuna wani muhimmin ci gaba a cikin shirin ta na sabunta birane da kare muhalli.

Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Asabar. Ya ce aikin ya nuna hangen nesan Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar wa mazauna jihar wuraren shakatawa masu tsaro, masu saukin shiga kuma masu kula da muhalli.

A cewar kwamishinan, wurin shakatawa da a baya ya kasance wurin ayyukan banza, yanzu ana sauya shi zuwa wani sabon fili na jama’a da aka tsara don inganta shakatawa, kiyaye muhalli da walwalar al’umma.

“Wannan aiki ya nuna hangen nesan Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar wa mazauna jihar wuraren shakatawa da filayen samun natsuwa, domin inganta lafiyar al’umma da jindadi,” in ji Hashim.

Ya ce aikin na daga cikin alkawarin gwamnatin na mayar da filayen jama’a dawo da wuraren shakatawa a fadin jihar, in da ya kara da cewa sake gyaran zai baiwa mazauna jihar wuri mai tsaro da kyau don hutu da tarukan jama’a.

Kwamishinan ya kuma ce sauya fasalin wannan wurin shakatawa na nuna kudurin gwamnatin na inganta rayuwar jama’a ta hanyar zuba jari a muhalli da shirye-shiryen sabunta birane.

Hashim ya yi fatan cewa za a kammala aikin nan ba da jimawa ba a bude shi ga jama’a, inda ya jaddada cewa gwamnati na ci gaba da himmatuwa wajen samar da wuraren more wa rayuwa da ke taimakawa wajen samun muhalli mai tsabta da lafiya.

Tun da farko dai, Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirinta na dawo da filayen shakatawa guda 10 a cikin birnin karkashin shirin “Green Mandate” da ke da nufin inganta kiyaye muhalli da kara jin dadin jama’a.

Watanni uku da suka wuce, Hashim ya bayyana cewa gwamnatin ta mayar da filaye da dama na jama’a da suka lalace ko aka sauya amfani da su, kuma ta fara sake gyara su.

Ya ce shirin na da nufin samar wa yara da iyalai sabbin filayen wasa da wuraren shakatawa masu kwanciyar hankali.

Gwamnatin ma na ci gaba da aikin sauya fasalin Nassarawa Park, inda ake mayar da wani bangare na wurin zuwa sabon fili mai dadi ada filin wasa, a matsayin wani bangare na shirin sabunta birnin da ake yi a jihar.

FB IMG 1782559815458 750x430FB IMG 1782559832596 1536x864FB IMG 1782559831609 1536x864

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here