Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, da Sanata Kabiru Garba Marafa, sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Kanar Bala Mande mai ritaya ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau babban birnin jihar a yau Lahadi.
Kanal Bala Mande ya ce, sun zauna sun kammala batun sauya sheƙar Yari da Marafa, kuma sun cimma matsaya na yin aiki don ci gaban Jam’iyyar.
“Dukkanmu mun amince mu yi aiki domin ci gaban jam’iyyar kuma PDP a jihar ta yi musu maraba da shigowa, Za mu tabbatar da adalci ga dukkan mambobinmu idan muka ci zaɓe a 2023.
“Za a sanar da ranar da za a yi gagarumar liyafa shigiwarsu jam’iyyar mu daga baya amma za mu aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma yayin taron masu ruwa da tsaki,” in ji Kanal Mande.
Sakataren yaɗa labarai na ɓangaren Yari, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin amma bai yi ƙarin bayani ba.
“Eh, gaskiya mun koma jam’iyyar adawa ta PDP, kuma wannan shi ne abinda zan iya cewa yanzu,” in ji Birnin Magaji.












































