Sheikh Hasina ta sake lashe zaben Bangaladesh karo na biyar

Hasina
Hasina

Firanministar kasar Bangaladesh, Sheikh Hasina ta sake lashe zaben kasar a karo na biyar.

Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan adawa suka kaurace wa zaben.

A cewar wani kwamishnan hukumar zaben kasar, jam’iyya mai mulki ta Awami League Party ta lashe fiye da kashi 50 na kujerun majalisar kasar.

Karanta wannan: Kasar Sweden ta kori bakin haure ‘yan Nigeria 36 daga Kasar

Rahotanni sun ce Md Atiqur da ke biye mata baya ya sami kuri’u dubu 6,999 sai kuma Mahabur Mollah da ya zo na uku da kuri’u 425.

Da yake sanar da sakamakon zaben da misalin karfe 8:30 na daren Lahadi agogon kasar, shugaban hukumar zabe Kazi Mahbubul Alam ya ce Sheikh Hasina ta yi wa abokan takarar ta fintinaku a babban zaben karo na 12.

Karanta wannan: Kano: Kotu ta janye umarnin kama wani jami’in hukumar hana fasa kauri

Zaben na bana na cikin zabukan da suka kafa tarihin kwanciyar hankali da lumana, in banda rahotannin tarwatsa masu zabe da kona wasu rumfuna da aka samu a wasu tsirarun gurare.

An dai gudanar da zaben Firanminista da kuma ‘yan majalisa 299 a zaben da ke da karancin ‘yan adawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here