Shugaba Tinubu ya amince da biyan Super Eagles Naira biliyan 12 na kudaden da suke bi

Gwamnatin Tarayya, albashin, ma'aikata,
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin Naira 35,000 da ta fara biyan ma’aikata domin rage radadin illar cire tallafin man fetur ga...

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya biya wasu kudade da kungiyar Super Eagles da sauran kungiyoyin wasannin kasar nan, ke bin gwamnatin tarayya.

A wata sanarwa da aka fitar a shafin X na cibiyar yada labaran Tinubu, a ranar Lahadi, ta ce biyan bashin ya hada da bashin albashin manyan masu horaswa na tawagar har na tsawon watanni 15, da kuma alawus-alawus ‘yan wasa mata, da kuma ‘yan kasa-kasa da shekaru 20 na tawagar kasa.

Karanta wannan: Tsohon dan wasan Super Eagles Justice Christopher ya rasu

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugaban kasa ya amince da biyan Naira biliyan 12 na baya-bayan nan ga kungiyoyin Najeriya na wasanni daban-daban, wadanda suka hada da Super Eagles da sauran su.

muna tafe da karin bayani………..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here