Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Kasa NITDA tace nan bada jimawa ba zata samar da cibiyar kere-keren fasaha ta zamani a Kano.
Shugaban hukumar Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin yaye dalibai 50 da cibiyar ENGAUSA TECH HUB, ta bawa hoto a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gaba daya daliban 50 da aka bawa horo a bangarori 2, ‘yan karamar hukumar Ringim ne.
Karanta wannan: NITDA ta bude Manhajar rijista dan bada horo ga ma’abota bunkasa fasahar sadarwa Milyan 1
Mutum 10 daga cikin su an horas da su ne akan gyaran wayoyin hannu na zamani, yayin da sauran mutum 40 din kuma aka horas da su akan yadda ake yin gini na zamani.
Da suka hadar da yadda ake hada lantarki a gida, da yadda ake hada daudaukar tsaro wato CCTV, sai yadda ake hada wuta mai amfani da hasken rana da kuma hada tauraron dan-Adam da sauran su.
Dukkan daliban sun rabauta da jakankunan kayan aiki da kudin su ya haura Naira dubu 100 a matsayin kyautar kammala karbar horo domin fara gudanar da sana’o’in su.
Karanta wannan: Hukumar ICPC ta fara gudanar da bincike kan zargin kammala digiri cikin mako 6 a Benin
Malam Abdullahi wanda ya yabawa Masarautar Ringim da kungiyar ‘Mafitar Ringim’ mai rajin samar da ayyukan yi ga al’umma tare da kokarin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa, ya kuma yaba wa cibiyar ta ENGAUSA TECH HUB bisa bayar da horon da harshen uwa ta yadda dalibai za su iya fahimta cikin sauki.
A nasa bangaren, wanda ya kafa ENGAUSA GLOBAL TECH HUB, Engineer Mustapha Habu Ringim ya ce tsarin horon da cibiyarsa ta dauka ya taimaka wajen sauwaka wa matasa sana’o’i masu sarkakiya.
Ya kuma ja hankalin iyaye da su dora ’ya’yansu akan hanyoyin da suka dace na amfani tare da bincike a shafukan sada zumunta domin samun damarmaki.
Kazalika ya yabawa dattawan masarautar biyu, IGP Hafiz Abubakar Ringim mai ritaya da JusticeTijjani Garba wanda ya dauki nauyin horar da dalibai 50 din.
Karanta wannan: Sarkin Katsina ya yi barazanar soke shirin AGILE a fadin Jihar
A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Ringim Alhaji Sayyidi Abubakar Mahmud wanda Chiroman Ringim Usman Sayyidi Mahmud ya wakilta bayan ya yabawa dukkan wadanda suka tallafawa shirin, ya bayyana alfahari da cewa dan masarautar Ringim ne ya kafa ENGAUSA.
Sarkin ya yabawa shugaban hukumar NITDA bisa yadda a koda yaushe yake bada goyon baya ga ci gaban masarautar.