Gwamnonin Najeriya sun bada miliyan 50 a raba wa mutanen da harin jirgin ƙasa ya rutsa da su

NGF 727x430 1 678x381 1
NGF 727x430 1 678x381 1

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya NGF, ta bada gudunmuwar Naira miliyan 50 ga gwamnatin jihar Kaduna domin raba wa fasinjojin da harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su.

Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya fitar a Abuja ranar Juma’a, ta ce, shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya jagoranci mambobin biyu na ƙungiyar zuwa jihar Kaduna.

Fayemi ya ce, tawagar ta je jihar ne domin jajanta wa gwamnati da sauran al’umma bisa harin da ɓata gari suka kai wa jirgin wanda yayi sanadiyyar jikkata da rasa rayuka baya ga fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

Shugaban na NGF, a lokacin da yake jawabi ga Gwamna Nasiru El-Rufai, ya jajanta wa jihar Kaduna da al’ummarta.

Haka kuma, Ya bayyana harin a matsayin babban abun tada hankali la’akari da yawan wadanda suka mutu da da kuma sauran abubuwan da suka faru.

Fayemi ya ce, “Abin takaici, ‘yan ta’addan sun jajirce wajen ganin sun yi garkuwa da wasu mutanen da suka tayar da hankulan jama’a, wanda ya jefa Kaduna cikin rudani.”

Da take jawabi tun da fari, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, ta bayyana harin da aka kai wa  jirgin a matsayin abun takaici, wanda ta yi addu’ar cewa neman jihar kada ta sake ganin makamancinsa.

Ta ƙara da cewa, tun da fari gwamna El-Rufai ya kasance a kan gaba wajen neman hanyoyin magance matsalar.

Mataimakiyar gwamnan ta kuma ce, ƙungiyar ta NGF da mambobinta sun kasance abokai na kwarai wadanda goyon bayan jihar ke da kima a garesu.

Ta kuma yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta wajen tallafawa jami’an tsaro a jihar.

“Wannan shi ne don cim ma aikin tabbatar da rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin aiki tuƙuru don nemo mafita mai ɗorewa ga matsalar, ta yadda ba za ta sake maimaita kanta ba,” in ji ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here