Jam’iyyar PDP ta sake ƙara wa’adin sayar da fom ɗin takara

PDP PDP
PDP PDP

Jam’iyyar adawa ta sake ta dai-daita jadawalinta ayyukanta na babban zaben baɗi.

PDP ta sanar da gyare-gyaren ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Mista Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja a daren Juma’a.

Ologunagba ya ce, an sauya sabuwar ranar rufe sayen fom ɗin takatar zuwa ranar Talata 19 ga watan Afrilu, yayin da aka tsawaita ranar karshe ta gabatar da fom ɗin zuwa ranar Laraba 20 ga watan Afrilu.

Ya ƙara da cewa, jam’iyyar ta gyara jadawalin ne domin ta cika kwanaki biyun hutun bukukuwan Easter kamar yadda gwamnatin tarayya ta sanar.

Ologunagba ya kuma ce, jam’iyyar ta sanya ranar Juma’a 22 ga watan Afrilu domin tantance masu neman kujerun majalisar dokoki.

Ya ƙara da cewa, an tsayar da ranar Litinin 25 ga watan Afrilu domin tantance ƴan takarar majalisar dokoki ta ƙasa yayin da ranar Talata 26 ga watan Afrilu za a tantance masu neman kujerar gwamna da kuma Laraba 27 ga watan Afrilun 2022 na masu neman takarar shugaban ƙasa.

“Duk sauran ranaku kamar yadda aka buga a baya ba su canzawa,” in ji shi.

Ya tunatar da masu neman kujerun majalisar dokoki da su mika fom ɗinsu zuwa sakatariyar jam’iyyar ta jiha.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here