Kano: Hukumar kula da gidajen yari da REMASAB sun ƙulla haɗin gwiwa don inganta tsaftar cibiyoyin gyaran hali

WhatsApp Image 2025 12 11 at 17.57.07 750x430 (1)

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya reshen Kano ta bayyana cewa tana ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumar kwashe shara ta jihar Kano domin inganta tsafta da ingancin hidima ga al’uhmma a cibiyoyin gyaran hali.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar MB Umar ya fitar, ta bayyana cewa shugaban sashen kula da ɗaurarru Musa Muhammad Kibiya ya kai ziyarar aiki ga shugaban hukumar REMASAB Dakta Muhammad S. Khalil domin tantance abin da za a inganta tare.

Taron ya mayar da hankali ne kan gano fannoni da za a yi haɗin kai a kansu tare da ƙirƙirar sabon tsarin aiki da zai inganta tsafta da ayyukan al’umma a cibiyoyin gyaran hali na jihar.

A yayin ganawar, Kibiya ya gode wa hukumar REMASAB bisa tarbar da ta yi tare da yabawa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda goyon bayan da take bayar wa wajen kyautata walwalar cibiyoyin gyaran hali.

Karanta: Gwamnatin Kano da hukumar NAGGW za su hada kai don inganta muhalli

Ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin biyu zai taimaka wajen ƙirƙirar shirye-shiryen hidima ga al’umma da za su rage cunkoso a cibiyoyin gyaran hali ta hanyar ba da hukuncin ladabtarwa ba tare da tsare mutane ba.

A nasa bangaren, Dakta Khalil ya bayyana ziyarar a matsayin mataki mai muhimmanci wajen samar da tsaftar muhalli da lafiyar cibiyoyin gyaran hali, tare da tabbatar da cewa hukumar tasa tana shirye ta ba da duk goyon bayan da ake bukata.

Haɗin gwiwar ya nuna himmar hukumomin biyu na inganta tsarin cibiyoyin gyaran hali a Kano tare da tabbatar da ingantattun shirye-shiryen hidima ga al’umma da za su amfani jama’a gaba ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here