Ministan harkokin waje Yusuf Tuggar ya bayyana cewa sojojin Najeriya da suka kasance cikin jirgin sama da ya saukar gaggawa a ƙasar Burkina Faso suna nan har yanzu cikin ƙasar, inda ake ci gaba da tattaunawa domin warware lamarin.
Tuggar ya bayyana hakan ne a birnin Abuja yayin wani taron haɗin gwiwa da ministan harkokin waje na ƙasar Benin Olushegun Bakari, inda aka yi bayani kan matsayin da sojojin suka samu kansu a cikinsa bayan saukar gaggawa.
A farkon makon nan ƙungiyar haɗaɗɗun kasashe yankin Sahel ta zargi wani jirgin da ke ɗauke da sojojin Najeriya goma sha ɗaya da karya dokar sararin samaniya ta Burkina Faso, lamarin da ya jawo tashin hankali a tsakanin ƙasashen yankin.
Ƙungiyar ƙasashen Sahel wadda ta ƙunshi Burkina Faso, Mali da Jamhuriyyar Nijar ta amince da baiwa mambobinta damar dakile duk wani jirgi da ya karya dokar sararin samaniyarsu, kuma lamarin ya zo ne daidai da lokacin da dakarun Najeriya suka kai harin sama a ƙasar Benin don dakile yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar.
Karin labari: Da ɗumi-ɗumi: Matuƙan jirgin saman sojin Najeriya sun tsira, yayin da jirgin ya yi hatsari a jihar Neja
Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa jirgin sama mai ɗaukar kaya na nau’in C-130 yana kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal lokacin da ya gamu da matsalar fasaha, wanda hakan ya tilasta masa sauka a garin Bobo-Dioulasso na Burkina Faso bisa ka’idojin tsaro da ka’idojin zirga-zirgar jiragen ƙasa da ƙasa.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun nuna cewa hukumomin Burkina Faso sun tsare jami’an sojin a farko kafin daga bisani su sake su, sai dai gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da shugaban mulkin soja na ƙasar Ibrahim Traoré domin tabbatar da an warware lamarin cikin gaggawa.
Tuggar ya tabbatar cewa sojojin suna nan a Burkina Faso tare da karin bayani daga hukumomin ƙasar Benin cewa saukar jirgin ba ta da alaƙa da taimakon da Najeriya ta bayar wajen dakile yunƙurin kifar da gwamnati a Benin, domin jirgin yana kan hanya zuwa Portugal ne lokacin da matsalar fasaha ta taso.













































