Katsina: Ɓata gari sun hallaka Kwamishina a gidansa

Rabe Nasir
Rabe Nasir

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da kisan gillar da wasu ɓata gari suka yi wa kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha da aikin ƙere-ƙere na jihar Alhaji Rabe Nasir.

Kwamishinan ƴan sandan Katsina Sanusi Buba ne ya tabbatar da hakan yayin da ya kai wata ziyara gidan marigayin da ke rukunin gidajen Fatima Shema a birnin na Katsina da maraicen Alhamis ɗin nan.

Kwamishinan ya bayyana cewa tuni rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta fara gudanar da bincike kuma suna dab da bankado masu hannu aika-aikar

“Kamar yadda kuka gani mun yi nasarar ɗakko gawar mamacin kuma mun kai ta asibiti kuma bincike ya yi nisa domin gano masu hannu a kisan tare da tabbatar da an cafke su.” inji Buba

Marigayi Rabe, tsohon jami’in tsaron DSS, ne da ya yi aiki da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati reshen birnin tarayya Abuja, kana ya wakilci yankunan Mani da Bindawa a majalisar tarayya na tsawon shekaru 4.

Kafin ɗaga likkafarsa zuwa mukamin kwamishina a gwamntin gwamna Aminu Bello Masari, ya kasance mataimaki na musamman ga gwamna a ɓangaren kimiyya da fasaha tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here