Fasahar Zamani ta sauya fannin sadarwa a Najeriya- Farfesa Pate

FB IMG 1662067376748 750x430

Fannin yaɗa sadarwar yaɗa labarai a Najeriya na samun gagarumin sauyi ne sakamakon samun ci gaba cikin sauri a fannin fasahar zamani da kuma sauye-sauyen yadda ake amfani da kafafen yaɗa labarai, a cewar Farfesa Umaru A. Pate Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere, a jihar Gombe.

SolaceBase ta ruwaito cewa Pate ya bayyana haka ne a yayin wani taron hukumar yaɗa labarai ta Najeriya NBC, da aka gudanar yau Talata a Abuja, inda ya gabatar da jawabi mai taken “Changing Broadcasting Dynamics in Nigeria”.

Ya nanata cewa tsarin al’ada da ayyukan cibiyoyin yaɗa labarai ana yin su ne ta hanyar juyin-juya halin fasahar Intanet da inganta fasahar sadarwa da fasahar zamani ta ICT.

A cewarsa, muhimman abubuwan da suka shafi yaɗa shirye-shirye ciki har da tattara labarai da shiryawa da kuma yaɗa labarai, a baya su na fuskantar matsala.

Ya lura da cewa yanzu Najeriya ta nutse cikin sabbin fasahohin zamani na kafofin yaɗa labarai, wanda ke da tsarin fasahar zamani da zamantakewa waɗanda ke ƙarfafa haɗin gwiwa, haɗin kai da ci gaba.

Ya kara da cewa, “Kafofin yaɗa labarai da ke tafiya a kan tsarin baya na cikin halin fuskantar barazana da matsaloli.

Da ya ke bayyana yanayin yaɗa shirye-shiryen Najeriya a matsayin abin da ke nuni da tattalin arzikin kasar da kuma yanayin zamantakewar al’umma, Pate ya gano kalubale da dama da ke ci gaba da gudana, da suka hada da rashin isassun kudade da tsohuwar fasahar zamani, inda ya koka bisa mamaya da kuma tsoma bakin ƴan siyasa musamman ma a kafafen yaɗa labai mallakin gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here