Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya saka dokar hana zurga zurga ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Lamurde daga yau, saboda rikice-rikicen da suka faru a wasu unguwanni a yankin.
Mai magana da yawun gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta lamunci tashin hankali ba, kuma ta umarci jami’an tsaro da su tabbatar da bin dokar.
Ya gargadi jama’a da su guji karya dokar, domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.
Haka kuma ya bukaci al’umma su taimaka da bayanai ga jami’an tsaro, tare da nisantar yada jita-jita.
Gwamnatin ta tabbatar da kudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da dawo da zaman lafiya a yankin.













































