Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, sannan ya aike da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zuwa kasar Ingila domin ya raka gawar magabacinsa zuwa Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar.
A cewar sanarwar, Tinubu ya ce Buhari ya rasu ne da misalin karfe 4:30 na yamma. a Landan bayan doguwar jinya.












































