Ministan wutar lantarki ya yi Allah wadai da harin da Sojoji suka kai kan Ikeja DiSCO

images 1 3 678x430

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi Allah-wadai da harin da jami’an rundunar sojin saman Najeriya suka kai kan shalkwatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja (IKEDC) ranar Alhamis.

Sanarwar da Bolaji Tunji, mai ba da shawara na musamman kan harkokin sadarwa ga ministan wutar lantarki ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin jikkatar wasu injina da dama, da lalata kayayyakin aiki.

Ya ce harin da sojojin saman Najeriya suka kai a kan cibiyar wuta ta Ikeja daya daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki a kasar nan abin takaici ne kuma abin damuwa ne.

A cewarsa, bangaren samar da wutar lantarki shi ne ginshikin tattalin arzikin kasa kuma ginshikin ci gaban kasa kuma duk wani hari da aka kai wa ababen more rayuwa hari ne ga dakile ci gaba da jin dadin al’ummarmu.

Karin karatu: Injin samar da hasken lantarki ya sake lalacewa

Ya ce an tsara kayayyakin aikin na Ikeja da ke yiwa miliyoyin ‘yan Najeriya hidima domin tabbatar da yadda ake rarraba wutar lantarki ga gidaje, asibitoci, makarantu, da masana’antu, gami da hukumomin sojoji.

Adelabu ya ce lamarin ya jawo koma baya a kokarin da ake na ganin an samu kwanciyar hankali da daidaiton wutar ba tare da katsewa ba, ya kara da cewa hakan na kawo cikas ga muradun al’ummar baki daya.

Ministan ya bukaci rundunar sojin saman Najeriya da ta tabbatar da cewa tana gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa tare da kula da jin dadin jama’a da kayayyakin more rayuwarsu.

A cewarsa, sojoji jami’ai ne masu muhimmanci a cikin al’ummar, kuma ba za a iya misalta rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro ba.

Adelabu ya kuma yabawa ma’aikata da mahukuntan kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja bisa jajircewar da suka yi wajen daidaita al’amura.

Ministan ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki da su yi aiki tare cikin lumana ta hanyar fifita bukatun al’umma, domin kuwa kalubalen da ake fuskanta a bangaren samar da wutar lantarki na da matukar illa, amma ba za a iya shawo kan su ba, inda ya ce idan aka yi hadin gwiwa da juna domin cimma manufar shawo kan matsalar.

Adelabu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su dage wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here