Injin samar da hasken lantarki ya sake lalacewa

Blackout

Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun ce sun fuskanci matsala a yau Juma’a daga babban layin wutar, abin da ya jawo jefa sassan ƙasar cikin duhu.

Kamfanin lantarki na Kedco – da ke bai wa jihar Kano da maƙobtanta wuta – ya nemi afuwar kwastomominsa cikin wata sanarwa.

“Muna masu baƙin cikin sanar da ku cewa an samu matsala a layin lantarki da misalin ƙarfe 2:00 na rana…abin da ya sa ba mu iya bai wa kwastomominmu wuta ba kenan,” in ji Kedco cikin wata sanarwa a shafukan zumunta.

Shi ma kamfanin lantarki na Ikeja Electric – mai bai wa jihar Legas da maƙobtanta wuta – ya fitar da irin wannan sanarwa. Sai dai dukkansu sun ƙi bayyana nau’in matsalar da aka samu, kuma ba su alaƙanta hakan da babban layin lantarki na ƙasa ba.

Akasari irin wannan na faruwa ne idan babban layin lantarki na ƙasa ya lalace, wanda yake yawan samun matsala.

Kazalika, kamfanin kula da rarraba wutar na gwamnati Transmission Company of Nigeria (TCN) bai ce komai ba game da matsalar.

Rashin wutar na yau ya shafi wasu sassa, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here