Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, daga jerin wadanda suka lashe zaben da aka gudanar a makon jiya.
A yayin INEC ke shirin mika wa wadanda suka ci zaben kujerar sanata da na majalisar tarayya takardun shaida, Aminiya ta lura hukumar ba ta sanya sunan Alhassan Doguwa ba a matsayin zababben dan Majalisar Tarayya na mazabar Doguwa/Tudun Wada.
Hakan kuwa na faruwa ne duk da cewa baturen zaben hukumar, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar cewa Alhassan Ado Doguwa na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’a 39,732, a yayin da babban abokin karawarsa, Yushau Salisu Abdullahi na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 34,798.
Amma a cikin jerin sunayen da INEC at fitar a ranar Litinin da dare na wadanda za a mika wa shaidar cin zabe, babu sunan Alhasannan Ado Doguwa.
Daga bisani hukumar ta bayyana cewa tursasa wa baturen zabenta aka yi ya sanar da sakamakon zaben da ke nuna dan majalisar ya lashe zaben ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Jaridar Aminiya tayi kokarin samun karin haske daga hukumar, amma hakan bai samu ba.
Sai dai sun kira Mataimakiyar Babban Jami’in Gudanarwa a Sashen Wayar da Kan Jama’a a Hedikwatar INEC da ke Abuja, Zainab Aminu Abubakar, ta waya, amma muka yi ta samun sabani. kuma har muka kammala hada wannan rahoton kuma tana kai wata wayar.












































