‘Yan bindiga sun nemi diyyar triliyan 40

'Yan Bindiga, sace, dalibai, makaranta
'Yan bindiga da suka sace wasu fadawan sarki a kauyen Gonin Gora na karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna ta arewacin Najeriya sun bukaci a biya su...

‘Yan bindiga da suka sace wasu fadawan sarki a kauyen Gonin Gora na karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna ta arewacin Najeriya sun bukaci a biya su fansar naira triliyan 40 fiye da kasafin kudin Najeriya da motoci kirar Hilux guda 11 da baburan hawa guda 150 kafin su saki mutanen.

A ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata ne ‘yan bidiga suka kutsa kai kauyen tare da yin awon gaba da mutanen.

Karin labari: Da Dumi-dumi: Majalisar dattawa ta dakatar da Abdul Ningi

A yammacin jiya litinin ne ‘yan bindigar suka fitar da wannan bukata da ta bar ‘yan Najeriya cike da mamaki, kasancewar kudaden da ‘yan bindigar ke bukata ya kusan ninka adadin kasafin kudin kasar baki daya.

Bukatar wadannan kudade na ban mamaki a matsayin kudin fansa na zuwa ne kwanaki hudu bayan da ‘yan bindiga suka kwashe daliban firamare da sakandaren Kuriga ta jihar Kaduna kusan 300.

Karin labari: Sheikh Gumi ya yi tayin shiga tsakani don ceto daliban Kuriga

Satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da fadada a Najeriya, inda ‘yan bindigar suka mayar da hankali kan dibar dalibai da kuma mata.

Bayanai sun ce cikin mako guda ‘yan bindiga sun sace mata da dalibai sama da 500 a arewacin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here