Dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya danganta ci gaba da tabarbarewar rashin tsaro a Najeriya da rashin ƙwarin gwiwar siyasa daga gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci bikin kammala bada horo da faretin fitar da sabbin jami’an tsaro 2,000 na Rundunar Tsaron kar-ta-kwana a Jihar Kano, inda ya kasance baƙo na musamman.
Ya tuno da gogewarsa a matsayinsa na tsohon Ministan Tsaro, inda ya bayyana cewa sojojin Najeriya na nuna bajinta sosai a ayyukan kiyaye zaman lafiya a ƙasashen waje, amma suna fuskantar ƙalubale a cikin gida sakamakon rashin cikakken goyon bayan siyasa.
Kwankwaso ya jaddada cewa ƙwarewar jami’ai da dakaru ta tabbata, amma abin da ake bukata a yanzu shi ne ƙudurin siyasa daga babban kwamandan rundunonin tsaro, ta hanyar samar da isasshen horo, ɗaukar sabbin jami’ai, kayan aiki, makamai da alburusai domin tinkarar rashin tsaro yadda ya kamata.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta shigar da horarrun jami’ai daga jihohin arewa kamar Kano, Katsina, Sakkwato, Kebbi da Zamfara cikin ayyukan tsaro na ƙasa, yana mai cewa Najeriya na buƙatar aƙalla jami’an tsaro miliyan ɗaya domin fuskantar barazanar tsaro a cikin gida da ma yankuna makwabta.
Ya ƙara da cewa ba a yankin Arewa maso Yamma kaɗai ake buƙatar ƙarin rundunonin tsaro ba, har ma a faɗin ƙasar baki ɗaya, domin taimaka wa sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen cika nauyin da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Duk da suka da ya yi wa gwamnatin tarayya, Kwankwaso ya bayyana fatan cewa shirin Rundunar Tsaron kar-ta-kwana ta Jihar Kano zai taimaka wajen dawo da tsaro, musamman a yankunan kan iyaka da ke fama da matsalolin rashin tsaro.













































