Bayan samun matsala ta farko, jirgin Marx Air mai dauke da alhazai 500 ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama  na Kano

KANO PILGRIM ARRIVE MADINA 2022 1 845x475 1
KANO PILGRIM ARRIVE MADINA 2022 1 845x475 1

Jirgin alhazan Jigawa wadanda suke kan hanyar su ta zuwa kasar Saudiyya ya yi saukar gaggawa a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano, hakan na zawo ne bayan jirgin ya samu matsala ta farko.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jirgin farko  mai dauke da alhazai 554 harda ma’aikatan jirgin 21 wanda ya tashi  daga filin jirgin sama na Dutse da misalin 4: 30 na dare a ranar Laraba ya sami matsala, bayan gyara matsala ne jirgin ya kara tashi da alhazan yau Alhamis.

Inda bayan sa’o’i uku da tashin nasa ya sake samun matsala a sararin samaniya na kasar Cameroun,  wanda hakan ya tilasta masa dawo wa Kano domin ya yi saukar gaggawa.

Manajan kamfanin jirgin na Max Air, Malam Bello Ramadan ya tabbatar wa da jaridar Solacebase cewa jirgin ya dawo Kano sakamakon matsalar da ya samu a sararin samaniyan Cameroun.

Majiyar mu ta shaidamana cewa Alhazan zasu cigaba da tafiya yau, bayan gyara matsalar da akai, kawai suna jiran umarni daga NCAA kafin tashin na su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here