Matawalle Ya Sace Motoci 17 da Kayan Ofis – Dare

Dauda Lawan Dare Zamfara PDP governorship candidate 718x430 1
Dauda Lawan Dare Zamfara PDP governorship candidate 718x430 1

Dauda Lawal Dare wanda ya karbi mulkin jihar Zamfara, ya zargi Bello Muhammad Matawalle da barin gidan gwamnati da kayan al’umma.

Ranar Alhamis Daily Trust ta rahoto Gwamna Dauda Lawal Dare ya na cewa Bello Muhammad Matawalle ya dauke motoci da kayan aiki da zai bar ofis. A ranar 29 ga watan Mayu aka rantsar da Dauda Dare a matsayin sabon Gwamnan jihar Zamfara.

Da aka yi magana da shi a gidan rediyon Vision FM da ke garin Gusau, sabon gwamnan ya ce babu abin da ya gada a baitul-malin Zamfara illa bashi.

Dare ya ce kafin Gwamna Matawalle ya bar ofis, sai da ya tattara motoci 17 da ake da su a ofishin Gwamna da ofishin Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara. Sannan Gwamnan ya ce ya iske an yi gaba da talabijin da na’urar dafa abinci da AC da kuma firji daga gidan gwamnati kafin rantsar da sabuwar gwamnati.

“Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya tafi da motoci 17 daga ofishinsa da na mataimakin gwamna, yana cewa motocin mallakarsa ne. Kai har kayan aiki na cikin ofis ba a kyale ba. Ta’adin da aka tafka ya wuce tunani, ban taba ganin rashin sanin ya kamata irin wannan ba. Amma idan aka yi tsari da kyau, ina mai tabbatarwa mutanen jihar Zamfara cewa za mu yi bakin kokarinmu wajen gyara kura-kuran.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here