Rundunar ƴan sanda ta karrama jami’inta saboda mayar da Dalolin da ya tsinta ga mai su

Police Honour 750x430 1
Police Honour 750x430 1

Rundunar ƴan sandan Katsina a ranar Juma’a, ta karrama wani ɗan sanda Nura Mande, wanda ya mayar da Dala 800 da suka ɓata ga mai su a Katsina.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan SP Gambo Isah, ya fitar ta ce, kwamishinan ƴan sandan jihar Idris Dabban, ya miƙa wa ɗan sandan takardar yabo da kuma Naira 30,000.

Ya ce, Mande yana bakin aiki a sansanin jin dadin alhazai na jihar Katsina inda ya gano Dala 800 na wata mata mai niyyar tafiya aikin hajji mai suna Hajiya Hadiza Usman.

“Yayin da yake gudanar da aikinsa a sansanin Hajji, PC Mande ya gano dala 800 a ƙasa sannan ya mayar wa Daraktan gudanarwa na hukumar, Alhaji Sada Salisu-Rumah.

“PC Mande ya bayyana cewa tsoron Allah ne ya sa ya mayar da kuɗin ga jami’in hukumar domin a mayar wa mai shi.

“Salisu-Rumah ya yaba wa ɗan sandan bisa kyawawan halayensa da kuma gaskiya,” ya kara da cewa.

A cewar Isah, kwamishinan ƴan sandan ya ji daɗin yadda Mande ya nuna gaskiya, ya kuma yi kira ga sauran ‘yan sanda da ke cikin rundunar da su yi koyi da shi.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaba wa jami’anta wadanda suka nuna gaskiya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here