ICAN ta rantsar da sababbin shugabanin ta

IMG 20220625 WA00132
IMG 20220625 WA00132

Cibiyar horar da akantotci ta kasa reshan jihar Kano ICAN, ta rantsar da sabon shugabanta na 41, tare da ‘yan majalisar zartarwa na cibiyar.

An gabatar da taron rantsarwar ranar juma’ a 24 ga watan June na shekarar 2022, a jihar Kano.

Yayin jawabin sa, sabon shugaban cibiyar Salisu Harun, ya yi alkawarin dorawa daga inda tsohon shugaban cibiyar ya tsaya.

“zan maida hankali wajan shirya bituci ga membobin mu, sanan kuma zan iya bakin kokari na don ganin cibiyar ta taimakawa yara ‘yan sakandire wadan da suka rubuta JAMB, amma basu sami damar shiga jami’ a ba, don ganin sun zama kwararun akantuci.”

A nasa bangaren, shugaban cibiyar horar da akantotci ta kasa ICAN, Malam Tijjani Musa Isah, wanda ya sami wakilcin Alh Nasiru Muhammad, ya yabawa tsofaffin shugaban nin cibiyar bisa jajir cewa da gudun mawar da suka bada har cibiyar ta kawo yanzu.

” ina fatan sa babbin shugabanin zasu maida hankali wajan habbaka cibiyar, don ganin an samar wa kasa Najeriya kwararun akantuci, sanan kuma ina kira a gareku da ku zama masu juriya, rukon gaskiya da amana yayin jagoranci ku.”

A nasa jawabin, Alh Shehu Muhammad Dan-kade, Sarkin shanun Kano, wanda shine uban taro. Ya yabawa cibiyar bisa gudun mawar da take bayarwa wajan hurar da akantuci a Najeriya, sannan kuma ya nemi sababbin shuwagabanin dasu dura daga inda wa ‘yan da suka gabacisu suka tsaya.

Yayin taron, cibiyar ta bada shedar girmamawa ga wadan su manyan mutane wandan da suke bawa cibiyar gudun mawa wa cibiyar da ganin ta cigaba. Alh Auwal Abdullahi Rano, na daya daga cikin wadan da suka karbe shaidar karramawar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here