Hukumar kula da harkokin jiragen sama ta ƙasa ta Najeriya ta gargaɗi kamfanonin jiragen sama na cikin gida da su daina ruɗar fasinjoji da ikirarin cewa mayar da kuɗin tikiti na ɗaukar makonni huɗu, tana mai tabbatar da cewa tsarin doka ya tanadi cewa dole a biya cikin kwanaki 14 kacal.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin, daraktan hulɗa da jama’a da kariyar masu amfani da jiragen sama na hukumar, Mika’il Achimugu, ya ce dole ne kamfanonin jiragen sama su bi ƙa’idojin da hukumar ta tanada ba tare da sabanin doka ba.
Hukumar ta bayyana cewa ka’idar ta na sashe na 19 na dokokin jukumar kula da harkokin Jiragen Sama na 2023 ta bayyana cewa lokacin da aka amince da mayar da kuɗin tikiti bai wuce kwanaki 14 ba, don haka babu wani kamfani da ke da ikon ƙirƙiro wani sabon tsari daban.
Achimugu ya shawarci fasinjojin da aka faɗa musu cewa kuɗin su ba za a mayar musu da shi sai bayan makonni huɗu su aika da ƙorafinsu zuwa michael.achimugu@ncaa.gov.ng, ifueko.abdulmalik@ncaa.gov.ng ko cpd@ncaa.gov.ng domin a gudanar da bincike.
Ya ƙara da cewa ba zai yiwu a ce ana son inganta harkar jiragen sama a ƙasar nan amma a lokaci guda ana yin abubuwa da ke rage wa hukumar iko da cutar da fasinjoji ba.
Hukumar ta kuma nanata cewa tana shirye ta fara fallasa da hukunta duk kamfanonin jiragen sama da suka karya ƙa’idojin da ta kafa domin kare hakkokin fasinjoji.










































