Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani soja mai suna Lans Kofural Akenleye Femi, wanda ake zargin ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa a cikin sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja.
Rahoton ya bayyana cewa lamarin mai cike da bakin ciki ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025, a cikin sansanin, abin da ya tayar da hankulan mazauna wurin.
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya reshen Birged ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ya ce marigayi Femi yana aiki a bataliya ta 221 da ke sansanin Wawa kafin rasuwarsa.
Binciken farko ya nuna cewa Femi yana bakin aiki a cikin sansanin lokacin da ya nemi izinin zuwa ya warware wasu al’amuransa na sirri, amma bai dawo bakin aiki ba.
Wannan ne ya sa jami’an soji suka je bincike inda suka tarar da gawarshi da ta matarsa a cikin ɗakinsu.
Rundunar ta bayyana cewa har yanzu ba a gano takamammen dalilin mutuwar tasu ba, amma an fara cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma dalilan da suka kai ga wannan lamari mai tayar da hankali.
Kyaftin Nwankwo ya ce an adana gawar mamatan, yayin da kwamandan birged ɗin, Birigediya Janar Ezra Barkins, ya tabbatar da cewa bincike zai gudana sosai kuma za a sanar da jama’a sakamakonsa.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana ta’aziyyarta ga iyalai, abokan aiki da abokanan mamatan tare da addu’ar samun rahama ga rayukansu.













































