Gwamnatin tarayya ta sa darusan koyar da sana’o’i a cikin manhajar karatun yan firamare da sakandare

plumbing

Gwamnatin tarayya ta sanar dasa sana’r gyaran gashi, aikin famfo, gyaran waya, sana’ar kwalliya da wasu sabbin sana’o’i/sababbin darussa guda 12 a cikin manhajar karatun boko.

Wannan ci gaban ya biyo bayan sauye-sauyen da ake yi a sassa daban-daban na tattalin arzikin Najeriya.

Wata sanarwa da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta {asa (NOA), ta fitar, ta ce an saka sabbin sana’o’in ne a cikin manhajar Ilimin Ilmi don inganta kwarewar dalibai da kuma samun aikin yi.

Sanarwar ta kara da cewa, sabbin darussan za su fara aiki ne daga watan Janairun 2025 ga daliban firamare da kananan sakandire a fadin kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here