Hisbah ta kama mutane 5 kan zargin yin auren da ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Kano Hisbah (1)

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa biyar bisa zargin shirya bikin aure ba tare da izinin iyaye ba, wanda ya saba wa ƙa’idojin addini da na doka.

Mataimakin kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a birnin Kano.

Ya ce cikin waɗanda aka kama akwai ango, amarya da kuma wasu mutum uku da suka tsaya matsayin wakilai da shaidu a wajen auren.

Rahoton ya nuna cewa auren an gudanar da shi ne da sadaki na naira 10,000 kacal, wanda ke ƙasa da adadin da shari’ar Musulunci ke amincewa da shi a matsayin mafi ƙaranci.

Aminuddeen ya ce wannan aure ya sabawa ƙa’idojin Musulunci da tsarin doka, inda hukumar ta kaddamar da bincike kan lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace.

Ya yi kira ga iyaye da su kula da harkokin ‘ya’yansu musamman a lamuran aure, tare da tabbatar da cewa ana bin ƙa’idar addini da doka wajen duk wata mu’amala ta aure.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here