Gwamnatin jihar Borno ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an kama Umara daya daga cikin ‘ya’yan Gwamna Babagana Zulum bisa zargin kashe wani dan kasar China a Indiya.
A cewar rahotannin kafofin sada zumunta, Umara, dalibi a wata jami’a a New Delhi, an rawaito cewa ya fasa kwalbar barasa a kan wani dan kasar Sin da ya nuna son wata mace da shima yake so a wani gidan rawa.
Da yake karyata rahotannin, Abdurrahman Ahmed Bundi, babban mataimaki na musamman ga gwamna Zulum kan sabbin kafafen yada labarai, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce babu daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan da aka kama ko aka tuhume shi da wani laifi, ko kuma ya shiga duk wani abu da ya sabawa doka a ko’ina.
Karin labari: Jirgin kasan Cargo daga Kano ya nufi Legas
Sanarwar ta bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan a lokacin fitar da bayanai.
Sanarwar ta ce: “Sashin yada labarai na Gwamnan Jihar Borno ya dauki hankulan mutane kan jita-jitar da ake yadawa cewa an kama dan Gwamnan Jihar Borno bisa zargin kashe wani dan kasar Indiya.
“An buga wannan mummunan labari ne a wani shafin yanar gizo mai suna “Dan Gwamnan Jihar Borno Ya Kashe Wani A Indiya—Siyasa.” Shafin ya yi ikirarin cewa Gwamnan ya kuma yi tafiya zuwa Indiya, yana kokarin yin amfani da matsayin diflomasiyya don warware matsalar.
Karin labari: Dikko Radda ya mika ragamar jihar katsina ga Mataimakinsa
“A bisa bayanan cewa Gwamna Babagana Zulum ya yi hutun wata daya a kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2024, daga baya kuma ya tafi kasar Masar domin halartar taron kungiyar ASUWAN na shekara-shekara a birnin Alkahira.
“Sashin Kafafen Yada Labarai na son fayyace tare da saita rikodin kai tsaye cewa shafukan yanar gizo sun yada labaran batanci ba tare da wani shaida na gaskiya ba” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen cin zarafi da musayar bayanai, musamman idan sun fito daga majiyoyi da shafukan yanar gizo da ba a tabbatar da su ba maimakon ingantattun kafafen yada labarai.
“Muna kira ga dukkan kungiyoyin kafafen yada labarai da su shiga aikin jarida na gaskiya da tabbatar da gaskiya tare da sanin illar cutarwa da rudani da yada labaran karya da ka iya haifarwa ga dangin Gwamna.”