Idris Dahiru, mazaunin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, ya ce an kashe ‘yan uwansa 34 a wani harin bam da sojojin Najeriya suka kai ta sama a yammacin Lahadi.
Aminiya ta ruwaito cewa sama da mutanen kauyen 90 ne suka mutu a lokacin da wani jirgin yakin sojojin Najeriya mara matuki ya afkawa taron jama’a na Mauludi. Sai dai rundunar sojin kasar ta yi nadamar tashin bam din, inda ta ce an kai harin ne kan ‘yan ta’adda.
Ya ce, “Bikin Mauludin da muke yi duk shekara ya ruguje ne sakamakon hare-haren da ba a zata ba. Bam na farko ya tashi ba tare da gargadi ba, ya kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da yara, wasu da bam din ya rutsa da su,” Dahiru ya shaida wa BBC Hausa.
“Yayin da muka garzaya don taimaka wa wadanda suka jikkata, jirgin ya dawo, inda ya sake tayar da bam na biyu, a wannan karon, da yawa daga cikin wadanda suka zo taimakon na cikin wadanda suka jikkata.
“Iyalaina kadai sun rasa yan uwa 34 a wannan bala’in.” ya kara da cewa