An Hallaka Wani Mutum Saboda Satar Kankana A Bauchi

32f58b82 7cef 4176 8ac3 209833ca15d9
32f58b82 7cef 4176 8ac3 209833ca15d9

An Hallaka wani mutum da ake zargi da satar kankana mai suna Ibrahim Hashimu, sakamakon dukan kawo wuka a kauyen Dallaji da ke karamar hukumar Warji a jihar Bauchi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Bauchi.

A cewar PPRO, ‘yan sanda sun cafke masu laifin.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa binciken farko farko da aka gudanar ya nuna cewa marigayin ya kutsa kai cikin wata gona mallakar wani Mohammed Garba inda ya yi awon gaba da ‘ya’yan kankana guda bakwai wanda kudinsu ya kai Naira 2,000, inda ya kara da cewa ana ci gaba da kwashe ‘ya’yan itatuwan da aka sace, sai mai gonar ya kama shi tare da hada baki, wasu kuma suka yi masa duka da sanduna, inda wanda ake zargin barawon ya samu rauni a ciki wanda ya kai ga mutuwarsa.

“Da samun rahoton, an dauki tawagar ‘yan sanda cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka dauki wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Warji domin kula da lafiyarsa, sannan aka tura su asibitin Cottage Hospital Gwaram LGA, jihar Jigawa, inda likitan ya tabbatar da mutuwarsa.” kakakin ‘yan sanda (SP), ya bayyana.

Ya ce an daure hannun mamacin da igiya, sannan Mohammed Daluta (24) da Ibrahim Mahmud (22) da Bashir Mahmud (18) da Abdullahi Mahmud (22) suka yi masa duka da sanduna.

Wakil ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan ya fusata da matakin da wadanda ake zargin suka dauka, inda a maimakon su kai karar ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da shi gaban kuliya, sai suka dauki doka a hannunsu. Ya bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) Bauchi domin gudanar da bincike mai zurfi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here