Kungiyar Dalibai ta kasa ta ne san ta kanta da batun zanga-zanga

NANS New 640x430

Shugaban kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta karyata ikirarin cewa tana shirin rufe manyan garuruwan kasar baki daya.

NANS ta ce ba ta sanar da hakan ba, ba ta kuma amince da irin wannan zanga-zangar ba, tana mai bayyana ikirarin a matsayin maras tushe.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na majalisar dattawa, Akinteye Babatunde, ya fitar a ranar Talata, NANS ya ce ikirarin ba ya nuna matsayi ko muradin kungiyarmu.

Sanarwar ta ce, “An sanar da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) game da jita-jita da labaran karya da ke yawo a bangarori daban-daban, wanda ke nuna cewa NANS na shirin rufe manyan biranen kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here