Jam’iyyar PRP ta yi watsi da taron da aka yi a Abuja, ta zargi ana yunkurin kwace iko da tsarin jam’iyya

PRP logo gold

Wani bangare na jam’iyyar PRP ya yi watsi da sakamakon taron kasa da aka ruwaito an gudanar kwanan nan a Abuja, inda suka bayyana shi a matsayin na bogi da suke zargin wani bangare da kokarin kwace jam’iyyar don muradun wasu manyan mutane gabanin zaben shekarar 2027.

Da suke jawabi a wani taron manema labarai a Kano a ranar Litinin, bangaren, karkashin PRP-Vanguard Collective, ya soki fitowar wani sabon shugaban jam’iyya na kasa daga abin da ya kira “bangaren Falalu,” yana mai jaddada cewa lamarin ya saba wa tsarin mulkin jam’iyyar da tushen akidarta.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu, ya soki Hakeem Baba-Ahmed musamman, wanda ya yi ikirarin cewa bai taba zama dan jam’iyyar PRP ba amma yanzu “yana ikirarin yana shugabantar al’amuranta.”

Daudu ya zargi sabon shugabancin da fara neman yan siyasa da aka watsar daga wasu jam’iyyun adawa, wani mataki da ya bayyana a matsayin cin amanar tsarin gurguzu na jam’iyyar.

“PRP ba ta sayarwa bace ga mai bayar mafi tsoka, Jam’iyya ce ta ma’aikata, masu ilimi masu ci gaba da talakawa masu wahala, ba mafaka ba ce ga ‘yan siyasa da suka gaza wadanda ke neman dama.” in ji Daudu.

Dauda ya zargi cewa wasu mutane a Kaduna wadanda ba su taba zama ‘yan jam’iyyar ba, yanzu suna ikirarin suna shugabantar al’amuranta, sun gayyaci ‘yan jam’iyyar ADC da sauran jam’iyyun da ke cikin rikici ba tare da tantancewa ba don cika PRP.

A cewar Dauda, “Yan Mafiyar Kaduna ba PRP ba ne. makiyan PRP ne. Su ne masu mulki. Su ne laima ta Arewa ta masu mulki. Ba sa adawa da cin zarafin mutane na jari-hujja.”

“Muna amfani da wannan dama don fada wa ‘yan Najeriya gaskiya, PRP ba ta sayarwa bace ga mai biya mafi tsoka, ko ga wadanda ke da idanu a kanta don saye. muna jan hankalin mai saye ya yi hattara, kada ya yi kasadar ajiyar kudinsa.” Dauda ya kara da cewa.

A cewar Daudu, jam’iyyar ta ci gaba da jajircewa ga akidun da aka kafa ta, wanda ya ginu a kan falsafar marigayi Mallam Aminu Kano, wanda ya fafata don kare hakkin ‘talakawa’.

Ya ce PRP-Vanguard za ta ci gaba da kalubalantar halaccin taron Abuja a kotu yayin da take tattara goyon baya a fadin ƙasar.

Bangaren ya kuma yi watsi da kiraye-kirayen sulhu a cikin jam’iyyar, yana tambayar tushen hadin kai a cikin abin da ya bayyana a matsayin “haramtacciyar hanya da cin amana ta akida.”

Ya yi gargadi game da mayar da PRP “mulkin mutum daya,” yana zargin cewa wasu mutane sun fi sha’awar samun kudi da tallafi na siyasa fiye da gina wata kungiya mai tushe a kasa.

Kungiyar ta yi amfani da wannan dama wajen sukar tsarin siyasa da tattalin arzikin Najeriya da ake da shi, tana bayyana shi a matsayin “tsarin jari-hujja na mulkin mallaka na zamani” wanda ya gaza wa talakawa tun bayan samun ‘yancin kai.

Ta kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tana zarginta da kara talauci da wahalhalun tattalin arziki.

“Gwagwarmayar ceto PRP daga hannun masu kudi wani bangare ne na fadan don ‘yantar da Najeriya daga cin zarafi,” in ji Daudu.

Ya sake jaddada jajircewar bangaren na bin hanyar shari’a, inda ta ke tattara jama’a daga kasa da shiga al’amuran jama’a, yana mai jaddada cewa PRP ta kasance “Jam’iyyar talakawa” kuma ba dandalin masu mulki ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here