INEC ta shirya gudanar da zaben cike gurbi a Kano–Kwamishinan Zabe

INEC
INEC

Hukumar zabe ta kasa INEC reshen Jihar Kano, ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zabukan cike gurbi a jihar.

Kwamishinan zaben jihar, Abdu Zango ne ya bayyana hakan ranar Talata lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a hedikwatar hukumar da ke Kano.

Karanta wannan: Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon mai taimakawa shugaban majalisar a matsayin kwamishinan hukumar zabe

Ya ce zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu zai gudana ne a mazabun majalisar dokokin jihar uku da suka hada Kunchi/Tsanyawa da Kura/Garun Malam, da kuma Rimin Gado/Tofa.

Ya ce tuni hukumar ta aike da kayan aikin ga dukkanin kananan hukumomin da abin ya shafa.

Zango ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a wato BIVAS a yayin sake zaben da nufin tabbatar da sahihin zabe.

Karanta wannan: Yan-sanda suna bincike akan sace shugaban karamar hukuma a Nasarawa

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa za’a gudanar da zaben cike gurbin cikin nasara.

Ya kuma yabawa kokarin ‘yan sanda na samar da tsaro da ake bukata kafin zaben da kuma lokacinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Hussaini Gumel, ya ce tuni rundunar ta sanya matakan tsaro domin tabbatar da gudanar da dukkan zabe cikin sauki a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Karanta wannan: Hukumar NUC ta magantu kan Farfesoshin bogi a Jami’o’i

Gumel, wanda CSP Hamma Abdullahi ya wakilta, ya ce ‘yan sanda za su fito a dukkan runfunan zabe domin baiwa mazauna kananan hukumomin 6 damar shiga zaben ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.

Ya gargadi shugabannin jam’iyyun siyasa da su ja hankalin magoya bayansu da su guji duk wani rikici na siyasa da kuma amfani da ‘yan daba a lokacin zaben.

Karanta wannan: Gwamnati ta dakatar da biyan mafi karancin Albashi-TUC

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya tuna cewa kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar 30 ga watan Satumbar 2023, ta bayar da umarnin sake zaben majalisar dokokin jihar a kananan hukumomin shida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here