Garo ya taya Ganduje murna cika shekaru 75 da haihuwa

Abdullahi Ganduje Ganduje 750x430

Mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kano a zaben 2023, Alhaji Murtala Sule Garo ya taya shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 75 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin gwanin jam’iyyar APC.

Garo a wani sakon tunawa da ranar haihuwa ta musamman ga tsohon gwamnan jihar Kano, a ranar Laraba, ya ce shugabancin Ganduje na hangen nesa ya samar da hadin kai wanda a karshe ya kai ga nasarar jam’iyyar a zabe hudu cikin biyar.

An haifi Dr Ganduje a ranar 25 ga Disamba 1949.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here