Tsohon firaministan Japan Shinzo Abe ya rasu, sa’a kadan bayan harbin shi da akai a wajan ralin kamfen.
An harbi Abe mai shekara 67 ne a yayin da yake jawabi a wajen wani gangamin yakin neman zabe a birnin Nara ranar Juma’a da safe.
An garzaya da tsohon fira ministan mai shekara 67 asibiti, an harbi Abe na farko bai same shi ba, sai harbi na biyu ne ya sami shi a baya, yayin da ya yanke jiki ya fadi kasa cikin jini.
Mista Abe na yin wani jawabin tallata wani dan takara ne, yayin wani gangamin yakin neman zabe a nara lokacin da harin ya auku – kuma shaidu sun ga wani mutum dauke da wata babbar bindiga.













































