
Alhaji Murtala Sule Garo, ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023 na jihar Kano, ya taya Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shugaban APC na ƙasa, murnar cika shekaru 75.
Garo ya yi alfahari da shugabancin Ganduje, wanda ya kawo haɗin kai da kuma nasarar jam’iyyar APC a cikin zabe hudu daga cikinbbiyar.
Ya bayyana Ganduje a matsayin shugaban da ya nuna juriya, mayar da hankali, da hangen nesa.
Garo ya yi addu’ar samun lafiya, albarka, da nasara ga Ganduje a dukkan abubuwan da zai yi.