Sarkin Kano na 15 Aminu Bayero ya nada Galadiman Kano

Alhaji Aminu Ado Bayero

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya amince da nadin Alhaji Sanusi Ado Bayero, wanda shine babban dan marigayi sarki Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano.

Wata wasika mai kwanan wata 21 ga Afrilun 2025 mai dauke da sa hannun babban jami’in gudanarwa Awaisu Abbas Sanusi, ta ce an amince da nadin ne bayan wani taro da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranta a ranar 16 ga Afrilun 2025.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa wasikar mai taken “Sanarwar izinin shiga Masallacin Fadar Nasarawa domin nada ku a matsayin Galadiman Kano,” ta gayyaci Sanusi Ado Bayero da ya gabatar da kansa a Masallacin Fadar da ke Gidan Sarki na Nassarawa, a ranar Juma’a 2 ga watan Mayun 2025, da karfe 9:00 na safe, domin karbar sarautar a hukumance.

Hakazalika, a ranar 9 ga Afrilun 2025, Sarki Sanusi II ya amince da karin girma ga Alhaji Munir Sanusi Bayero daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano.

Labari mai alaƙa: Sarki Sanusi ya nada sabon Galadima, Wambai, da sauran muhimman mukamai a masarautar Kano

An mika amincewar ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Matawallen Kano, Aliyu Ibrahim Ahmad.

Wannan nadin ya nuna yadda masarautar Kano ke kara tabarbarewa bayan dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki, bayan tsige shi a shekarar 2020.

A kwanakin baya ne Sarki Sanusi ya nada Galadiman Kano bayan rasuwar Alhaji Abbas Sanusi, Marigayi Galadima.

Yayin da sarakunan biyu ke gudanar da mulki iri daya, shugabancin gargajiya a Kano na fuskantar rashin tabbas da ba a taba ganin irinsa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here