Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke kasar Ingila ta lashe gasar Premier League din kasar sakamkon chasa Tottenham da ci 5-1 a filin wasanta na Anfield.
A mintuna 45 din farkon wasan yan wasan kungiyar ta Liverpool Luis Diaz, Alexis Mac Allister da kuma Cody Gakpo suka ci kwallaye hudu.
Sai dai daga bisani dan wasa Mohammed Salah ya zura kwallo na biyar hakan yasa ya ci kwallo 28 a kakar wasanni ta bana a gasar.
sai dai dan wasa Destiny Udogie ya ci gida hakan yasa Tottenham ta tsira da kwallo daya a wasan.
Karon farko kenan bayan shekaru 35 da kungiyar ta Liverpool ta gudanar da murnar daukan gasar a gaban magoya bayanta, ko a shekarar 2020 ba tayi murnar daukan gasar ba a gaban magoya bayan nata sakamakon annobar COVID 19 (dpa/NAN)