Gwamna Fintiri ya dakatar da wani hakimi bisa zargin almundahana

Ahmadu Fintiri 750x430

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ya dakatar da hakimin Daware, Alhaji Hassan Ja’afaru.

Ana bincikar Ja’afaru, Hakimin Daware a karamar hukumar Fufore, inda aka same shi da laifukan almundahana, rashin gudanar da mulki, tauye sha’anin tsaro da sauran laifuka.

A wata wasika mai kwanan watan 25 ga Afrilu, 2025 mai dauke da sa hannun babban sakatare mai kula da harkokin masarautu, Adama Mamman, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi, ya umurci hakimin da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa ga sakataren gundumar.

Wani bangare na wasikar ya kara da cewa, “Bayan wasu korafe-korafe da ake yi a kan ku na gazawar shugabanci, cin hanci da rashawa, tabarbarewar tsaro, kwace gonaki da rashin samar da zaman lafiya wanda ya sa duk wasu al’amuran gargajiya suka kasance cikin rashin kula, sakamakon rashin zaman ku a yankinku, don haka ne Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya umarce ni da in ba ku umarnin dakatar da ku daga ofis”.

“Saboda haka, an bukaci ku mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunku ga magatakardar gundumar har zuwa wani mataki na gaba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here