Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane hudu da suka hada da wani sabon ango, bayan rasuwar matarsa a karamar hukumar Sule Tankarkar da ke jihar.
SolaceBase ta ruwaito cewa an bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar ranar Lahadi.
Shisu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar, yayin da jami’in ‘yan sanda reshen Sule Tankarkar ya kaddamar da bincike kan zargin da ake yiwa angon da abokansa.
Sakamakon binciken farko ya nuna angon mai suna Auwal Abdulwahab dan shekara 20 ya hada baki da wasu abokansa guda uku – Nura Basiru mai shekaru 20 da Muttaka Lawan mai shekaru 20 da Hamisu Musa mai shekaru 20 duk a kauyen Tungo da ke gundumar Albasu domin tilasta wa amaryarsa yin lalata da su.
Karin karatu: Gwamna Fintiri ya dakatar da wani hakimi bisa zargin almundahana
A yayin yunkurin, amaryar wadda rahotanni suka ce ta samu rashin jituwa da mijinta kan alakar aure tun lokacin daurin aurensu, ta tayar da hankalinta lamarin da ya kai ga mutuwarta.
Da samun rahoton, tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO ta garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe gawar zuwa babban asibitin Gumel, inda wani likita ya tabbatar da rasuwar ta. Daga baya aka mika gawar ta ga iyalanta domin yi mata jana’iza.
Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake zargin za su iya fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da laifin hada baki da kuma kisan kai.
Ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, CP AT Abdullahi, ya bayar da umarnin a mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) da ke Dutse domin gudanar da bincike mai zurfi.
Kuma za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.













































