Gwamnatin Zamfara ta gargadi mazauna jihar da su guji amfani da lambobin wayar Gwamna Bello Matawalle ba tare da izini ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata ta hannun Zailani Bappa, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan wayar da kan jama’a, yada labarai da sadarwa a Gusau.
“Manufar mai mai girma gwamna ta bayar da lambar wayarsa ga jama’a shi ne don su sanar da shi kan lamuran tsaro da kuma al’amuran da suka shafi ci gaban jihar.
“Haka kuma yana sanya ido a shafukan sada zumunta da na yanar gizo don jin ta bakin mutane.
“Wannan shi ne don kara tsara abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba kamar yadda jama’a ke so da kuma burinsu.
“Duk da haka, wasu masu sakaci suna amfani da wannan dama da hanyar da bata dace ba, inda suke sanya lambar a shafukan da basu dace ba, kuma ba tare da izini ba,” in ji shi.
Ya ce ya shawarci mutane da su guji kai wannan lamba duk wani dandalin sada zumunta ba tare da izini ba.












































