Majalisar Dattawa ta tsawaita aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021 zuwa ranar 31 ga Mayu

download 3
download 3

Majalisar dattawa ta kara tsawaita aiwatar da kasafin kudin shekarar 2021 daga ranar 31 ga Maris zuwa 31 ga Mayu.

Wannan ya biyo bayan la’akari da wani kudirin doka don Gyara Dokar Kasafin Kudi na 2021.

An karanta kudirin ne a zaman majalisar a ranar Talata a karo na farko da na biyu da na uku bayan dakatar da doka ta 78(1).

Shugaban Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi ne ya dauki nauyin kudirin.

Da yake jagorantar muhawara kan kudirin, Abdullahi ya ce an zartar da dokar kasafin kudin a shekarun baya a tsakiyar shekara, inda aka saba aiwatar da shi har zuwa shekara mai zuwa.

Abdullahi ya ce tsawaita wa’adin kasafin ya zama wajibi bisa la’akari da bukatar kammala ayyukan da ake daf da kammalawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here