Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin daurin shekaru 24 a gidan kaso ga wani Mubarak Bala, wanda ya yi ikirarin cewa babu Allah.
Wanda aka yanke wa hukuncin, wanda shi ne shugaban kungiyar Humanist Association of Nigeria ya tabbatar da cewa ya yi kalaman batanci ga Allah da kuma Annabi Muhammad (S.W.A).
Mubarak ya yi suna a kafafen yada labarai a shekarar 2020 inda aka kama shi a gidansa da ke Kaduna bisa laifin zagin Allah da kuma tunzura jama’a.
Bala, wanda ya shafe kusan shekaru biyu a gidan gyaran hali, ya tabbatar da aikata lefin a gaban kotu a ranar Talatar, inda aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume 18.
Yayin da yake rokon kotu da ta yi adalci, Bala ya yi alkawarin ba zai sake maimaita wannan kalami na batanci ba, yana mai cewa bai san zai haifar da irin martanin da ta samu lokacin da ya raba su ba.
Tun da farko, alkalin kotun, Mai shari’a Farouk Lawan, da lauyan wanda ake tuhuma, James Ibori, sun yi kokarin gamsar da shi kan laifin da ya yi, amma wanda ake tuhumar ya dage cewa ya san abin da yake yi kuma ya ci gaba da rokonsa.
Dangane da karar da ya shigar, alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari.
Tun da farko lauyan ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa na da matsalar tabin hankali, inda aka yi masa jinya a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke Kano.













































