Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar jihar murnar shiga sabuwar shekarar musulunci na ranar Lahadi 1 ga watan Al-Muharram 1446 Bayan Hijra.
Abba, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a shafinsa na Fesbuk.
“Ina taya al’ummar jihar Kano murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.
Karin labari: Hukumar NDLEA ta kama wani mai hidimar kasa da fataucin kwayoyi a Kano
“Mu yi amfani da wannan rana, da kuma ranar hutu a ranar Litinin don yin tunani game da shekarar da ta gabata da kuma yin ayyuka masu amfani.
“Gwamnatinmu, a nata bangaren, za ta ci gaba da aiwatarwa da bullo da tsare-tsare da za su baiwa ‘yan kasa damar dogaro da kai,” in ji Abba.