Sabon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), reshen Ungogo, a jihar Kano, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe, ya bayyana shirinsa na shekaru biyu masu zuwa.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi a karshen mako, Gwadabe ya bayyana jindadinsa ga daukacin mambobin reshen bisa amincewar da suka yi masa na tafiyar da harkokin reshen.
Daga nan sai Barista Gwadabe ya gabatar da wani ajanda mai kunshe da abubuwa bakwai na inganta harkokin shari’a a cikin reshen.
Karin labari: “Ina taya al’ummar jihar Kano murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci” – Gwamnan Kano
SolaceBase ta tabbatar da cewa ajandar ta hada da inganta bin doka da oda, jindadin mambobi, karfafa kyakkyawar alaka da masu ruwa da tsaki, da ci gaban ababen more rayuwa, da dai sauransu.
Ya kuma jaddada cewa reshen a karkashin shugabancinsa zai yi kokarin kafa ofishi kamar takwaransa na Kano.
A nasa jawabin tsohon shugaban reshen Muhammad Jibril ya yabawa mambobin reshen da suka ba shi damar yin shugabanci na tsawon shekaru biyu.
Karin labari: ‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna
A lokacin da yake aiki, ya bayyana cewa reshen ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, wanda ya hada da samar da kayan aiki na sakatariya kamar sabuwar na’ura mai kwakwalwa da na’urar daukar hoto.
Bugu da kari, ya bayyana cewa reshen ya halarci taron majalisar zartarwa na kasa (NEC) sau biyu.
Malam Jibril ya mika sakon fatan alherinsa ga sabon shugaban.