‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan jarida 2 da iyalansu a Kaduna

'Yansandan, Najeriya, ‘Yan sanda, stabbatar, sace, ‘yan jarida, iyalansu, Kaduna
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta tabbatar da yin garkuwa da wasu ‘yan jarida biyu da iyalansu a Kaduna da misalin karfe 10:30 na daren...

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta tabbatar da yin garkuwa da wasu ‘yan jarida biyu da iyalansu a Kaduna da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, wanda ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ce jami’ansu na kokarin ganin cewa wadanda abin ya shafa sun samu ‘yanci kuma ba a samu rauni ba.

Ya ce: “Mun tura jami’an mu cikin daji idan ana zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: An shawo kan matsalar katsewar wutar lantarki a Najeriya

“Wadanda abin ya rutsa da su su ne shugaban kungiyar ‘yan jarida ta NUJ Council na jihar Kaduna, AbdulGafar Alabelewe da wasu ‘yan uwa guda 3 da aka yi garkuwa da su a daren jiya a Danhono 2, a garin Millennium City, na Kaduna.

“Haka zalika, an yi garkuwa da wakilin jaridar Blueprint Abdulraheem Aodo tare da matarsa ​​a wuri guda. AbdulGafar Alabelewe kuma shine wakilin jaridar kasa.” kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here