An samu daidaiton dawo da daukewar wutar lantarki a Najeriya.
Idan ba’a manta ba jaridar SolaceBase ta bayyana katsewar wutar lantarki a Najeriya karo na hudu da yammacin ranar Asabar, abinda ya jefa al’ummar kasar cikin wani yanayi na daukewar haske.
Saidai a halin da ake ciki yanzu labari ya fita an samu nasarar shawo kan matsalar, kowanne lokaci daga yanzu za’a ci gaba da samun wutar lantarki a sassan kasar kamar yadda sanarwa ta fita daga Abdulazeez Abdullahi shugaban sadarwar kamfanin.
Karin labari: An sake samun katsewar wutar lantarki karo na 4 a Najeriya
Ya ku abokan ciniki masu daraja.
Muna nuna alhininmu da sanar da ku cewa katsewar wutar lantarki da ake fama da ita a cikin jihohin mu ya samo asali ne daga tushen Grid.
Matsalar ta faru ne da misalin karfe 3:10 na yamma.
Za’a dawo da wutar lantarki da zaran an kunna wutar lantarki ta ƙasa.
Muna neman afuwarku bisa kasancewar daukewar wutar.
Sa hannu:
Abdulazeez Abdullahi
Shugaban, Sadarwar Kamfanin.
6/07/2024